Nijar

An soma kidayar kuri'u bayan kammala zaben Nijar zagaye na 2

Yadda jami'an hukumar zaben Nijar suka soma kidayar kuri'u bayan kammala zabe zagaye na biyu
Yadda jami'an hukumar zaben Nijar suka soma kidayar kuri'u bayan kammala zabe zagaye na biyu AFP / ISSOUF SANOGO

An fara kidaya kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar Jamhuriyar Nijar zagaye na biyu da ya gudana yau a rumfunan zabe 25,978, cikin da’irori 266 inda aka fafata tsakanin Mohamed Bazoum na PNDS TARAYA da Mahamane Ousmane na RDR Tchanji.

Talla

Daga birnin Yamai, Rakiya Arimi Niamey ta aiko mana da rahoto kan soma kidayar kuri'un.

Rahoto kan soma kidayar kuri'u bayan kammala zaben Nijar zagaye na 2

Wanda ya samu nasara a wannan zabe a tsakanin tsohon shugaban kasa Mahaman Ousmane na jam'iyyar RDR Canji da kuma Bazoum Muhammad na PNDS Tarayya, zai zama shugaban Jamhuriyar Nijar na 10 bayan Hamani Diori da Seyni Kountche da Ali Saibou da Mahamane Ousmane da Ibrahim Bare Mainassara da Dauda Malam Wanke da Mamadou Tandja da Salihou Djibo da kuma shugaba mai barin gado Mahamadou Issofou.

Zaben na Nijar na zuwa ne yayinda dakarun kasar ke cigaba da kokarin murkushe hare-haren ‘yan ta’adda akan iyakarta da Najeriya daga barin kudu maso gabashi, sai kuma iyakar ta da Mali dake yankin kudu maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI