Nijar-Zabe

Rikici ya barke a Nijar bayan nasarar Bazoum a zaben shugaban kasa

Mahukuntan Jamhuriyyar Nijar sun sanar da girke tarin jami'an tsaro don kawo karshen rikicin da ya biyo bayan nasarar Bazoum.
Mahukuntan Jamhuriyyar Nijar sun sanar da girke tarin jami'an tsaro don kawo karshen rikicin da ya biyo bayan nasarar Bazoum. AFP - ISSOUF SANOGO

Sakamakon zaben Nijar ya haddasa tashin hanklai tsakanin magoya bayan Bazoum Mohamed wanda hukumar zaben kasar ta bayyana a wanda ya lashe zaben da kuma dan takarar jam’iyyar adawa Ousmane Mahaman da shima a bangaren guda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.

Talla

Tun a jiya Alhamis al’amura suka fara tsananta a Jamhuriyar ta Nijar bayan da rikicin siyasar  ya dau wani sabon  salo, inda masu zanga zanga  suka kona gidaje da shagunan jama’a cikin har da gidan wakilin sashen Faransanci na rfi a birnin Yamai.

Rikicin na zuwa ne kwanaki 4 bayan gudanar da zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar da hukumar zaben kasar CENI ta ce dan takarar jam’iyar da ke mulkin kasar Mohamed Bazoum, ne ya lashe kashi 55.75 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada, sakamakon da dan takarar Adawa tsohon shugaban kasar  Ousmane Mahaman ya kalubalanta.

Kawo yanzu Mutum biyu hukumomi suka tabbatar da mutuwarsu a mabanbantan zanga-zangar da ke ci gaba da zafafa a Jamhuriyyar Nijar, karon farko da kasar ke gani a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.