NIjar-Siyasa

Shugaban Nijar ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou. AP - Gael Cogne

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issofou ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim dake dauke da Dala miliyan 5 saboda yadda yaki amincewa ya sauya kundin tsarin mulkin domin cigaba da zama a karaga kamar yadda wasu shugabannin kasashen Afirka ke yi.

Talla

Gidauniyar tace shugaba Issofou ya gudanar da jagoranci na gari wajen shawo kan matsalolin da suka addabi jama’a irin su talauci, yaki da ‘yan ta’adda da kuma fari.

Shugaban kwamitin bada kyautar Festus Mogae yace shugaban yayi nasara rage yawan jama’ar kasar dake fama da talauci daga kashi 48 da aka sani shekaru 10 da suka gabata zuwa kashi 40.

Mogae yace duk da kalubalen dake gaban shugaban, Issoufou ya cika alkawarin da ya yiwa al’ummar nijar na shatawa kasar makoma mai kyau wajen shirya zaben da ya samar da wanda zai gaje shi, wanda shine irin san a farko tun bayan lokacin da kasar ta samu ‘yanci daga kasar Faransa sama da shekaru 60 da suka wuce.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen Afirka ta Yamma suka yi kaurin suna wajen sauya kundin tsarin mulkin kasashen su domin tsawaita zaman su a karaga.

Mo Ibrahim mai gidauniyar dake karrama shugabannin Afrika da suka hakura da zarcewar dindindin kan karagar mulki.
Mo Ibrahim mai gidauniyar dake karrama shugabannin Afrika da suka hakura da zarcewar dindindin kan karagar mulki. ASSOCIATED PRESS - ALASTAIR GRANT

Ita dai wannan kyauta da Gidauniyar Mo Ibrahim ke baiwa tsoffin shugabannin, ana bada ita ne sakamakon Nazari kan shugabanci da mutunta kundin tsarin mulki da kuma tabbatar da ginshikan dimokiradiya.

Shugaba Issofou ne zai zama na 6 da zai karbi kyautar wanda aka dade ba’a bada ita ba saboda rashin samun wanda ya dace.

Wadanda suka lashe kyautar zasu karbi Dala miliyan 5 da aka tsara a cikin shekaru 10, tare da kuma Gidauniyar Dala 200,000 na iya rayuwar su.

Shugaban mai barin gado ya godewa Gidauniyar Mo Ibrahim saboda wannan karramarwar da ta masa, wadda yace zata dada karfafa masa gwuiwa wajen goyan bayan cigaban dimokiradiya a da shugabanci na gari a Nijar da kasashen Afirka.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.