Nijar - Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe mutane 58 a Nijar

Taswirar Jamhuriyar Nijar dake nuna yankin Tillaberi mai fama da hare haren ta'addanci.
Taswirar Jamhuriyar Nijar dake nuna yankin Tillaberi mai fama da hare haren ta'addanci. AFP

Yayin wani hari da ‘yan ta’adda suka kai kan wasu kauyuka dake kusa da garin Banibangou na jihar Tillaberi a yammacin kasar Nijar ranar Litinin,mutane  58 sun rasa rayukansu.

Talla

Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun tare fararen hular ne a kan wasu hanyoyi biyu da ke hada Banibangou, Chinagoder da kuma Dareydey, yayin da suke dawowa daga cin kasuwar garin na Banibangou kusa da iyakar Nijar da Mali.

Majiyar tace lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda maharan suka tsayar da motar da mutanen ke ciki, suka kuma bindige su har lahira, kafin daga bisani su bankawa motar wuta.

Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar yayin karbar horo daga dakarun. kasar Amurka a cikin Burkina Faso.
Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar yayin karbar horo daga dakarun. kasar Amurka a cikin Burkina Faso. U.S. Africa Command - Richard Bumgardner

A cikin watan Disambar shekarar da ta gabata, kungiyar ta’addanci da ake kira ‘Grand Sahara’, ta dauki alhakin harin da aka kai wa wani barikin soji da ke garin Chinagoder, inda suka kashe sojojin kasar ta Nijar fiye da 100.

Zalika a cikin ‘yan watanni da suka biyo baya, wasu ‘yan bindigar sun kai hari a kan kauyukan Tomabangou da kuma Zaroumdarey tare da kashe fararen hula fiye da dari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.