Gwamnatin Nijar ta tura karin sojoji Banibangou

Kwararowar bakin zuwa yankin Abala a Arewacin Tillabery na zuwa bayan rikicin da ke ci gaba da tsananta a Mali sakamakon rashin shugabanci a wasu sassan kasar.
Kwararowar bakin zuwa yankin Abala a Arewacin Tillabery na zuwa bayan rikicin da ke ci gaba da tsananta a Mali sakamakon rashin shugabanci a wasu sassan kasar. RFIHAUSA/Awwal

Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta ce an tura karin sojoji don tabbatar da tsaro a yankin Banibangou, bayan da ‘yan bindiga suka kashe fararen hula 66 kamar yadda sabbin alkaluma suka nuna, wadanda suka dawo daga cin kasuwa a ranar litinin da ta gabata.

Talla

Ministan cikin gidan kasar Alkache Alhada, wanda ya ziyarci garin na Banibangou don jajantawa jama’a dangane da mummunan hari, y ace jami’an tsaron da aka tura za su rika zagayawa a cikin kauyuka da kuma kasuwanni domin kare rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.

 

Jami'an tsaro a wasu yankunan  da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery
Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery RFI

Ministan cikin gidan ya ce nan ba da jimawa za a tura karin jami’an tsaro 500, wadanda ke gab da kammala samun horo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.