'Yan bindiga sun kashe mutane 60 a Nijar
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 60 sun rasa rayukansu a wani farmakin da 'yan bindiga suka kaddamar kan wasu kauyuka da ke Jamhuriyar Nijar a kusa da kan iyakar kasar da Mali mai fama da tashe-tashen hankula kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar wa AFP.
Majiyoyin sun ce, wasu mutane dauke da muggan makamai sun dirar wa kauyukan akan babura , inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.
Sun kai harin ne a kauyukan Intazayene da Bakoarate da Wistane da kuma wasu garuruwa makota a cewar shaidun gani da ido.
A ranar 15 ga wannan watan na Maris, mutane 66 suka rasa rayukansu a wannan yankin na iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu