An zabi Seyni Oumarou a matsayin shugaban majalisar dokokin Nijar
Wallafawa ranar:
An zabi Alhaji Seini Oumarou a matsayin shugaban sabuwar majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, zaben da ‘yan adawa suka kaurace wa.Shi dai Seini Omar ya fito ne daga jam’iyyar MNSD Nassara wadda ta mara wa zababben shugaban kasar Bazoum Mohamed baya.
Kaurace wa kada kuri’ar zaben sabon shugaban majalisar dokokin, na matsayin karba umarni daga Alhaji Mahaman Ousman dan takarar adawa da ke cigaba da bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da shugabancin kasar.
Oumarou ya samu kuri’u 129 daga cikin 129 da Yan majalisu suka kada kamar yadda aka gudanar, yayin da yan adawa suka kauracewa zaben.
Seyni Oumarou wanda ya jagoranci gwamnatin MNSD Nasara da ta rike mulkin Nijar tsakanin shekarar 1999 zuwa 201 a matsayin Firaminista ya marawa Jam’iyyar PNDS baya wajen ganin ta samu nasarar zaben da akayi zagaye na biyu, bayan ya zo na 3 a zagayen farko.
Shugaban majalisar dokokin ya fito ne daga kabilar Djerma dake Yankin Tillaberi, yankin dake fama da hare haren yan bindiga saboda iyakar da yayi da kasashen Mali da Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu