Nijar - Ta'addanci

An kawo karshen taron kasashen G 5 a Jamhuriyar Nijar

Zauren taron kungiyar G 5 a Djamena
Zauren taron kungiyar G 5 a Djamena AFP - MICHELE CATTANI

A birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, an kawo karshen taron tattaunawa domin samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel da kuma zagayen tafkin Chadi, taron da hukumar tattalin zaman a Nijar wato HACP ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dimkin Duniya wato UNDP-PNUD.

Talla

Domin shawon kan matsalolin tsageranci da ta’addanci a yankin tsakiyar sahel da wuraren tafkin Chadi ne hukumar karfafa zaman lafiya HACP ta Nijar tare da hadin gwiwar kungiyar PNUD suka gudanar da wani taron nazari a birnin yamai, wanda ya samu halartar manyan masana kan zaman lafiya.

Rakia Arimi daga birnin yamai ta aiko da rahoto.

Taron Ministocin kasashen G 5
Taron Ministocin kasashen G 5 RFI/Salem Mejbour

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.