Nijar-Bazoum

Ba zan yi sulhu da 'yan ta'adda ba- Zababben shugaban Nijar

Zababben shugaban Nijar Mohamed Bazoum.
Zababben shugaban Nijar Mohamed Bazoum. © RFI

A zantawarsa ta farko tun bayan da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohamed ya shaida wa RFI cewa, ba shi da niyar shiga tattaunawa da ‘yan ta’adda da ke kai wa kasar hare-hare, a daidai lokacin da mahukunta a makociyar kasar wato Mali ke cewa a shirya suke su fara tattaunawa da kungiyoyin da ke ikirarin jihadi. 

Talla

Kuna liya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da RFI ta yi da zababben shugaban na Nijar.

 

Ba zan yi sulhu da 'yan ta'adda ba- Zababben shugaban Nijar

 

Zababben shugaban ya tabo batutuwa da dama da suka hada da cin hanci da rashawa da talauci da kuma siysar Nijar har ma da batun zaben da ya ba shi nasara.

Bazoum ya kuma jaddada muhimmancin karfafa wa mata guiwa domin samun ingantaccen ilimi, yana mai kokawa kan yadda ake yi wa 'yan mata auren wuri a kasar.

Sabon shugaban ya bayyana shirinsa na musamman don ganin mata sun dauki dogon lokaci suna karatun boko, abin da zai hana su auren wuri a rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.