Nijar-Juyin Mulki

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da yunkurin juyin mulkin kasar

Shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou na.
Shugaban Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou na. RFI

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi yau da asuba kwana biyu kafin kawo karshen mulkin shugaba Mahamadou Issofou da kuma rantsar da sabon shugaban kasa Bazoum Mohammed.

Talla

Mai magana da yawun gwamnati Abdurrahmane Zakari yace daren jiya zuwa wayewar gari yau 31 ga watan Maris dakarun gwamnati sun yi nasarar murkushe wani yunkuri da ya kira na matsarota masu neman mayar da dimokiradiya baya na kifar da gwamnatin kasar.

Sanarwar ta ce zaratan sojin kasar sun yi nasarar murkushe yunkurin da kuma hana masu juyin mulkin isa fadar shugaban kasar dake birnin Yammai.

Rahotanni yau da safe sun sanar da samun harbe harbe daren jiya da manyan makamai kusa da fadar shugaban kasa Mahamadou Issofou wanda kasashen duniya suka yabawa wajen jagoranci na gari da kuma kin sauya kundin tsarin mulki kamar yadda wasu shugabannin kasashen Afirka keyi domin cigaba da zama a karagar mulki.

Wannan ya sa shugaban mai barin gado ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim mai dauke da Dala miliyan 5, yayin da ake saran ya mika mulki ga zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed ranar juma’a mai zuwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.