Nijar

Rahoto kan halin da ake ciki a Nijar bayan yunkurin juyin mulki

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyyar Nijar.
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyyar Nijar. Issouf SANOGO AFP

A daren 30 zuwa 31 na watan maris aka kai harin juyin mulki ga fadar shugaban kasa Issoufou Mahamadou wanda saura kwanaki 2 da ya sabka daga karagarsa na mulkin kasar Niger.

Talla

Sojoji sun yi “yunkurin juyin mulki” a daren Talata zuwa Laraba wajen karfe 3 na dare a birnin Yamai,  kasar Nijar, a cewar majiyoyin da ke kusa da iko, "Wannan rukunin sojoji bai samu ya ci nassarar zuwa fadar shugaban kasa ba, lokacin da masu gadin fadar shugaban kasar suka mayar da martani"

Abdourahamane Zakari kakakin gwamnati ya tir da wannan al’amarin.

Mazauna anguwar fadar shugaban kasar a Yamai, sun shaida mana cewa  harbe-harben manyan bindigogi da kananan makamai ne ya tadasu da barci wanjen karfe 3 na dare

''Halbe haben nan sun tsoratar da ni, tunda a gani na za’a kai mana hari ma, balle ma a wannan al’ammuran dake faruwa komi na iya faruwa, ni har na ga an yi juyin mulkin''.

''Lokacin da abun ya fara ina cikin gari, iyayena suka kirani, nan da nan na yi tsammanin juyin mulki ne, wasu na gani cewa wasan koykoyo ne dan a hana gerin gwanon nan, har yanzu bamu san mike faruwa ba''.

''Ni na aza yan ta’adda ne suka shigo anguwarmu, amma yau da safe na ji ana cewa ai wai juyin mulki ne aka yi yunkurin yi wanda bai ci nassara ba.ni ban yarda ba da cewa zuyin mulki ne''.

''Al’amarin tsaron ya sa tsammanin harin yan ta’adda kafin in san cewa halbe halben nan daga fadar shagaban kasa yake, ina ganin yan kasar niger basu da bukatar wannan, muna fatan zaman lafiya da lumana''. 

A cewar jaridar le gardien capitaine gourouza sani saley, wanda ke kula da tsaron kamfanin jirgin sama na Yamai ne kan gaban wannan yukurin juyin mulkin da ba ta ci nassara

A cewar wata majiyar tsaro, a yanzu haka jami'an tsaro suna nemansa ruwa a jallo, an kame wasu daga cikin mukarrabansa.

'Yan sanda sun mamaye anguwar shugaban kasa, amma a wasu wuraren birnin, al’amarin ya saba laraban inda mutane suke ci gaba da harkokinsu kamar babu abin da ya faru. Wannan "yunkurin juyin mulkin" ya zo ne dab da ranar da za’a rantsar da sabon shugaban da aka shirya yi a ranar Juma'a 2 ga watan Aprilu  a Yamai,

Mu tunatar da ku cewa juyin mulki 3 ne kasar Niger ta fuskanci, Seyni Koutché  1974 ( Diori Hamani ya kayar da shi), Ibrahim Baré Mainassara watan Janeru na 1996  (Mahame Ousmane ya kayar da shi), Salou Djibo a watan febrairu na 2010 (ya kayar da Mamdaou Tanja)

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake yunkuri ko shirya juyin mulki ga shugaba Issoufou Mahamadou.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.