Nijar-Arlit

Kamfanin Cominak ya daina aiki a Nijar bayan shekaru 43

Wani bangare na kamfanin Cominak a yankin Arlit na Jamhuriyar Nijar.
Wani bangare na kamfanin Cominak a yankin Arlit na Jamhuriyar Nijar. AFP PHOTO PIERRE VERDY

Kamfanin Cominak da ke hako makamashin Uranium ya kawo karshen ayyukansa tare da sallamar illahirin ma’aikatansa sama da 1,400 a Jamhuriyar Nijar. Kamfanin ya kwashe tsawon shekaru 43 yana hako ma'adinai a garin Arlit da ke jihar Agadez.

Talla

Tun a cikin shekarar 2019, kamfanin ya fara bayyana shirinsa karara na kawo karshen aikinsa a yankin na Agadez

A yayin zantawa da sashen Hausa na RFI, Boubacar Haruna da ya shafe shekaru 19 yana aiki a kamfanin ya ce,

Mun jima da jin zancen sai ga shi an wayi gari aikinmu ya dakata.  gaba daya Arlit ya girgiza.
Babu wani aiki da muka Sani sai wannan. korar ma'aikata dubu 1 da 400 za ta jefa rayuwarmu cikin wahala. Inji Haruna.

Kamfanin ya yi alkawarin bai wa kowanne daga cikin ma'aikatansa na dindin da yawansu bai wuce 600 ba kudin da suka tashi daga miliyan 20 zuwa 50 kowannansu.

Almou Ghabda na Kungiyar Kananan Ma'aikatan, na ganin cewa, ya kamata a sama wa korarrun ma'aikatan aiki.

Gwamnati ta fifita kamfanonin  cikin gida ta yadda za su dauki matasan aiki, da kuma saukaka musu yanayin rayuwa.”

Wani al'amari da kamfanin ke fatan warwarewa,  shi ne tsaftace yankunan da guba ta yi wa illa a Arlit, inda ya ware kudi har Cfa biliyan 194 don yin aikin.

Almoustapha Alhassan na Kungiyar Kare Muhalli, Aghirman ya ce,

Ina matukar jin tsoron guba radio-activite ta yi wa mazauna Arlit illa sosai. Tun da kasan ita gubar tana dadewa a cikin jikin mutun har tsawan shekaru  

Tuni gwamnatin Nijar ta danka wa wani kamfanin lasisin tono Uranuim a wani wurin na daban wanda kuma a halin yanzu ya jinkirta aikinsa don jiran tashin farashin makamashin saboda a yanzu darajarsa ta yi kasa.

Wajen hakar uranium a Arlit, Jamhuriyar Nijar
Wajen hakar uranium a Arlit, Jamhuriyar Nijar REUTERS/Joe Penney/File Photo

 

Tuni China ta nuna sha'awarta ta ci gaba da harkar Uranium din a Nijar domin zamanantar da bangaren wutar lantarkinta.

Labarin rufe Cominak ya dauki hankalin hukumomin da ke sanya ido kan lamurran makamashin nukiliya a duniya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.