Nijar-Bazoum

Manyan kalubalen da ke gaban sabon shugaban Nijar Bazoum Mohamed

Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum. Issouf SANOGO AFP

Yayin da yau aka rantsar da Bazoum Mohammed a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, mun yi nazari kan wasu daga cikin manyan kalubalen da ke gaban sa kamar haka.

Talla

Tsaro – matsalar tsaro na daga cikin manyan kalubalen da ke gaban sabon shugaban kasar ganin yadda Nijar ke fuskantar matsaloli daga bangarori daban daban.

Nijar na fama da matsalar masu ikrarin jihadi akan iyakokin ta da Mali da kuma Burkina Faso tun daga shekarar 2012 da aka kifar da gwamnatin Mali.

Akalla mutane sama da 300 'yan bindigar da ke kai hare hare akan iyakokin kasar suka hallaka a cikin wannan shekara kadai.

Daga bangaren kudu maso gabashin kasar kuwa, rikicin boko haram ya yi sanadiyar hallaka mutane da dama, abinda ya haifar da matsalar 'yan gudun hijirar da ke tserewa daga Najeriya suna samun mafaka a Nijar.

Nijar na samun taimakon sojin kasashen Amurka da Faransa wajen horar da dakarun ta da kuma basu taimakon kayan aiki, yayinda take hadin kai da sojojin Najeriya da Kamaru da Chadi wajen tinkarar mayakan.

Talauci – Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen da ba suyi iyaka da teku ba, abinda ke shafar tattalin arzikin ta, yayin da kashi biyu bisa uku na yankin kasar ke fama da hamada.

Alkaluma sun nuna cewar da dama daga cikin jama’ar kasar kusan miliyan 22 da rabi na fama da talaucin da ake dangantawa da yawan haihuwa ganin yadda kowacce mace guda ke haihuwar yara akalla 7, abinda ake hasashen cewar yawan jama’ar kasar na iya kaiwa miliyan 70 a shekarar 2050.

Nijar na daya daga cikin kasashen da ke gaba gaba wajen samar da sinadarin uranium da kuma man fetur, sai dai faduwar farashin su na shafar kudaden shigar da take samu.

Sama da kashi 40 na arzikin kasar na zuwa ne daga noma wanda sama da kashi 80 na al’ummar kasar suka dogara akai duk da barazanar da suke fuskanta sakamakon sauyin yanayi.

Cin hanci – jamhuriyar Nijar ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da juyin mulki wadanda suka dakushe cigaban ta tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Sau 4 soji ke jagorancin juyin mulki a kasar kuma na baya bayan nan shi ne wanda aka yi a watan Fabararirun shekarar 2010 wanda ya kawar da shugaba Tandja Mahamadou daga karagar mulki.

Rashin biyan ma’aikatan gwamnati albashin da ya dace na haifar da matsalar cin hanci da rashawa, abinda ya sa yanzu haka ake gudanar da bincike kan batar makudan kudaden da aka ware domin sayen makamai da ake zargin sun bata.

Cin zarafi – Zanga zangar 'yan kasa lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Mahamadou Issofou sun haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro.

A lokacin gwamnatin da ta bar karagar mulki an kama Yan Jaridu da dama kuma an gurfanar da su a gaban kotu saboda zargin aikata laifi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.