Nijar-Bazoum

Rahoto kan bikin rantsuwar Bazoum Mohamed a matsayin shugaban Nijar

Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum. Issouf SANOGO AFP/File

Yau 2 ga watan Aprilun shekarar 2021 ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Niger Bazoum Mohamed wanda aka zaba ta hanyar demokaradiya, kuma zai jagoranci kasar tsawon shekaru 5 akan karagar mulki. Rahoton wakiliyarmu Rakia Arimi Niamey

Talla

Karo na farko a tarihin kasar Niger da shugaban kasa wanda aka zaba ta hanyar demokaradiya ya mika mulki ga sabon shugaban kasa wanda shima aka zaba ta hanyar demokaradiya kuma a jam’iya guda.

Shugaba Bazoum Mouhamed ya rantse gaban dubbunnan al'ummar kasar da tarin baki daga kasashen ketare da suka halarci bikin rantsuwar a yau.

'' Ni Mohamed Bazoum, zababben shugaba a karkashin doka, mai rantsuwa akan littafi mai tsarki cewa zan mutunta tare da tabbatar da cewa ana mutunta kundin tsarin mulkin kasa'' 

''Zan gudanar da ilahirin ayyukan da suka rataya a wayana, ba zan taba cin amanar kasa ba, zan tabbatar da cewa na bautawa jama'ar kasa, idan kuwa na kaucewa saba wannan rantsuwa to a shirye na ke na fuskanci fushin doka''.

''Bayan karbar wannan matsayi daga wanda ya gabace ni ina sane da irin kalubalen da ke gabana, a cikin shekaru biyar masu zuwa zan yi aiki tukuru domin kyautatawa yanayin tsaro, bunkasa ilmi, kiwon lafiya, samar da wadataccen abinci, ruwan sha, muhalli, wutar lantarki da kuma gina hanyoyi domin amfanin al'umma''.

''Zan tabbatar da cewa adalci da kuma samar da daidaito a tsakanin ilahirin 'yan kasa, zan kasance zababben shugaba ga ilahirin al'ummar kasar Nijar''. 

Daga bangaren mahalar bikin murna da fatan alheri, Tsohon sarkin Kano daga tarayyar Najeriya Muhammadu Sunusi na II ya taya al'ummar nijar murna tare da bayyana kakkarfar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

An haifi Bazoum Mouhamed a shekarar 1960 a garin bilabirin N’gourti na jihar Diffa, sau 5 ya ke zama dan majalissan garin Tesker, Shugaban diflomasiyyar Nijar sau 2, ya kuma rike mukamin minista ciki har da na jiha a 2016, ministan cikin gida, na tsaron jama'a, da na al'adu da kuma na harkokin addini har zuwa 2020.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.