Nijar- Bazoum

Rashin imanin 'yan ta'adda ya ketare duk wata iyaka - Bazoum

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum. Issouf SANOGO AFP/File

Sabon shugaban Nijar Bazoum Muhammad da yayi rantsuwar kama aiki, ya yi tur da mayakan dake kai hare-haren ta’addanci a sassan kasar wadanda ya zarga da aikata laifukan yaki.

Talla

Rantsar da sabon  shugaban na Nijar a ranar Juma’a 2 ga watan Afrilu ya kafa tarihin zama karo na farko da gwamnatin farar hula ta mikawa wata mulki a tsawon shekaru 60 da Jamhuriyar ta Nijar ta shafe bayan samun ‘yancin kai daga Faransa.

Yayin jawabinsa na farko bayan karbar jagoranci daga tsohon shugaba Mahamadou Issofou, shugaba Bazoum ya caccaki kungiyoyin ‘yan ta’adda, wadanda ya ce rashin imaninsu ya ketare duk wata iyaka, la’akari da kisan gillar da suka yiwa fararen hula masu yawan gaske, abinda babu shakkah ya tabbata laifukan yaki ne suka aikata.

Sabon shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Muhammad.
Sabon shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Muhammad. © Reuters

Nijar na fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi dake biyayya da kungiyar Al’qaeda ko IS wadanda ke ketarawa cikin kasar ta bangaren yammaci daga Mali da Burkina Faso, sai kuma Kungiyar Boko Haram dake kaddamar da nata hare-haren bayan shiga kasar dta bangaren kudu maso gabashi daga Najeriya.

Alkaluman baya bayan nan da hukumomi suka tattara sun nuna cewar mutane fiye da 300 ‘yan ta’adda suka kashe a yammacin Nijar, daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Sabon shugaban Nijar mai shekaru 61, zai shafe shekaru 5 kan wa’adin jagorancin kasar, bayan samun nasarar lashe zaben da ya gudana zagaye nabiyu a watan Fabarairu da kashi 55.6, sakamakon da abokin hamayyarsa Mahamane Ousmane yake kalubalanta a kotu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.