NIjar-Siyasa

Yau juma'a ake rantsar da Bazoum Mohammed a Jamhuriyar Nijar

Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed
Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed Niger Search

A yau Juma’a 2 ga watan Afrilu ake rantsar da zababben shugaban jamhuriyar Nijar Bazoum Muhd kan karagar shugabancin kasar da zai shafe wa’adin shekaru 5 yana jagoranta.Bikin rantsuwar dai na zuwa ne bayan nasarar lashe zaben shugabancin Nijar zagayea na biyu da ya gudana a ranar 21 ga watan Fabarairu da ya gabata, inda ya samu kashi 76 cikin 100 na kuri’un da aka kada. 

Talla

An haifi Mohamed Bazoum ne a 1960  a yankin Diffa cikin kabilar Ouled Slimane, karamar kabila a Jamhuriyar Nijar. A shekarar 1980  ya fita karatu a jami’ar  Cheikh Anta Diop dake birnin Dakar na kasar Senegal, inda ya kammala tare da nasarar samun takardar shaidar ilimin Falsafa.

Ya dawo gida Nijar bayan samun nasarar kammala karatun, inda ya fara koyarwa. Kafin ya zama mamba a cikin babbar  kungiyar malaman makaranta ta kasar  Nijar,  daga nan kuma  ya zama daya daga cikin shuwagabannin kungiyar kwadago ta kasa, wace a karkashinta ya halarci zauren babbar mahawarar  kasa a 1991.

Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed
Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed Niger Search

Yan watanni bayan taron Mohamed Bazum ya kafa jam’iyar PNDS Tarraya tare da shugaba Mahamadu Issoufou

Mohamed Bazoum, ya samu nasarar shiga gwamnati a matsayin sakataren kasa a ofishin ma’aikatar harakokin waje yana dan shekaru 30 . Haka kuma ya zama dan majalisar dokoki. Ya rike mukaman mnistoci da dama. Ya kuma zama ministan harakokin waje a tsakanin 2011 zuwa 2015.

Kafin ya rike ministan kasa, haka kuma na cikin gida da kuma tsaron  lafiyar jama’a daga watan Avrilun 2016-2020.

Tsakanin waddanan mukamai 2 da ya rike  daga 2015 zuwa  2016 ya zama ministan kasa a fadar shugaban kasa, inda ya kula da aikin ganin an sake zaben shugaba Mahamadu Isufu a karo na 2.

A ranar 31 ga watan maris 2019 ne Jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki  da yake shugabanta tun cikin 2011 ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta a zaben shugabancin kasar na 27 ga watan Disemba 2020 da ya cimma nasarar kaiwa a zagaye na 2 da aka yi a ranar 21 ga  wata na fabrairu 2021.Ya kuma lashen zaben shugabancin kasar na Nijar,wanda hakan ne karo na farko da wani zabbaben Shugaba farrar hula ya mika mulki zuwa wani shugaban farrar hula a Nijar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.