Nijar - Chadi

Nijar: Ana zargin sojojin Chadi da aikata fyade

Sojojin Chadi yayin atasaye a yankin Diffa dake Jamhuriyar Nijar.
Sojojin Chadi yayin atasaye a yankin Diffa dake Jamhuriyar Nijar. © REUTERS/Joe Penney

Hukumar kare hakkin dan adam ta Jamhuriyar Nijar ta bukaci gudanar da bincike kan zargin  sojojin Chadi da yiwa wasu mata fyade a kasar ciki har da wata yarinya mai shekaru 11.

Talla

Dakarun Chadin da ake zargin na Jamhuriyar Nijar ne inda suke taimakawa wajen yaki da ‘yan ta’adda.

A binciken sharar fagen da ta wallafa a ranar Juma’ar da ta gabata, hukumar kare hakkin dan adam ta Nijar din, ta bayyana samun hujjojinta kan zargin dakarun na Chadi da yiwa wasu mata uku fyade ciki har da karamar yarinya da kuma wata mai juna biyu, daga binciken lafiyar da ta samu a tsakanin 31 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilun da muke.

Rahoton ya ce sojojin na Chadi sun keta haddin matan ne a kan idanun mazajensu, wadanda ke tsare da bakin bindiga. Zalika adadin matan da aka ci zarafin nasu ya zarce wanda ya bayyana, sai dai mafi akassrinsu sun ki bayyana kansu ne, saboda fargabar fuskantar tsangwama. Zalika akwai wasu matan akalla 5 da dakarun na Chadi suka yi yunkurin yin musu fyaden amma suka samu sa’ar tserewa daga gidajensu.

Baya ga aikata fyade, ana kuma zargin sojojin na Chadi da cin zarafin mutane tare da kwace musu dukiya a yankin Tera dake yammacin Nijar kusa da iyakar kasar da Burkina Faso, inda suke da sansani.

Cikin watan Fabarairun da ya gabata Chadi ta aike da dakarunta dubu 1 da 200 zuwa yankunan dake kan iyakokin Nijar, Mali da kuma Burkina Faso,  domin karin karfi ga sojojin Faransa dubu 5 da 100 da hadin gwiwar dakarun sauran kasashen dake yakar kungiyoyin mayaka masu alaka da Al’Qaeda.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.