Nijar - Najeriya

Nijar za ta tattauna da Najeriya kan makomar 'yan gudun hijira

Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed
Zabebben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed © Niger Search

Sabon shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya ce zai shiga tattaunawa da gwamnatin Najeriya domin mayar da ‘yan gudun hijirar da suka tserewa matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriyar domin samun mafaka a kasar ta Nijar.

Talla

Matakin dai na daga cikin alkawuran da sabon shugaban kasar na Nijar ya dauka a lokacin da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi.

Yayin jawabin da ya gabatar, Bazoum yak oka kan yadda ta’addanci ya zamewa Jamhuriyar Nijar babban bala’i duk da cewa sansanonin ‘yan ta’adda, da ma shugabanninsu na wajen kasar.

Fassarar kalaman sabon shugaban Nijar Bazoum Mohamed
Fassarar kalaman sabon shugaban Nijar Bazoum Mohamed

Yayin ranstuwar kama aiki a ranar 2 ga watan Afrilu, sabon shugaban Nijar Bazoum Muhammad da ya zargi mayakan dake kai hare-haren ta’addanci a sassan kasar da aikata laifukan yaki.

Nijar na fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi dake biyayya da kungiyar Al’qaeda ko IS wadanda ke ketarawa cikin kasar ta bangaren yammaci daga Mali da Burkina Faso, sai kuma Kungiyar Boko Haram dake kaddamar da nata hare-haren bayan shiga kasar dta bangaren kudu maso gabashi daga Najeriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI