Nijar-Azumi

Wasu tsiraru sun ki amincewa da daukar azumin Ramadana a Nijar

Wasu yara yayin karatun Al-Qur'ani mai girma.
Wasu yara yayin karatun Al-Qur'ani mai girma. AP - Rahmat Gul

Yau Talata, galibin al’ummar musulmin Jamhuriyar Nijar sun fara azumin watan Ramadana, Sai dai kamar kowace shekara, a bana ma an samu wasu tsiraru mutanen da ba su dauki azumin ba saboda sabanin ra’ayi kan tsayuwar jinjirin watan.Tuni kungiyoyin addini suka yi gargadi kan duk wani yunkuri na bujire wa umurnin hukuma.Daga Agadez ga rahoton wakilinmu Umar Sani.