Nijar-Gobara

Gobara ta kashe dalibai 20 a Jamhuriyyar Nijar

Gobarar ta tashi ne a azuzuwan da aka gina da kara da ciyawa a Jamhuriyar Nijar
Gobarar ta tashi ne a azuzuwan da aka gina da kara da ciyawa a Jamhuriyar Nijar © ANP

Yara 20 sun rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a ajujuwan makarantar firamare ta gwamnati da ke babban birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Talla

Shugaban ‘yan kwana-kwana Sidi Mohamed ya ce, ibtila’in ya rutsa da yaran ne  bayan sun makale a cikin rumfunan  azuzuwan na ciyawa.

Mohamed ya ce, ma’aikatan agaji sun kai dauki nan take tare da kashe wutar, amma  gobarar ta tsananta sosai a  cewarsa, lamarin da ya sa kananan yaran suka kasa tsira da rayukansu.

Rahotanni sun ce, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Talata, a daidai lokacin da daliban ke daukar darasi a azuzuwan.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin tashin gobarar.

Tuni Firaministan Nijar, Ouhoumadou Mahamadou ya ziyarci makarantar domin isar da ta’aziyar rashin wadannan dalibai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.