Nijar-Bazoum

Shugaban Nijar Bazoum ya fara ziyarar aiki a Najeriya

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a Najeriya.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a Najeriya. © Buhari Sallau

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya fara ziyarar aiki a Najeriya inda zai gana da shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar sa ta farko zuwa kasar tun bayan rantsar da shi da aka yi.

Talla

Rahotanni sun ce shugaban ya samu kyaukyawar tarba daga shugaba Buhari da wasu manyan jami’an sa da suka hada da ministan Abuja Muhammad Bello da kuma gwamnonin Jihohin Sokoto da Zamfara da Yobe da Kebbi da Borno.

Bayanan dake zuwa daga fadar shugaban Najeriya dake Abuja tace shugabannin biyu na ganawar sirri yanzu haka, yayin da ake saran shugaba Buhari da bakon nasa suyi buda baki da yammacin yau.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed a Najeriya
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed a Najeriya © Buhari Sallau

Bazoum Mohammed ya gaji tsohon shugaban kasa Mahamadou Isssofou a matsayin shugaban Jamhuriyar Nijar sakamakon nasarar da ya samu a zaben da aka yi a Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.