Nijar

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci shirin tattaunawar kasa da sakin fursunoni

Sojojin Nijar yayin sintiri a birnin Niamey lokacin zabe, 23 ga watan Fabarairu 2021.
Sojojin Nijar yayin sintiri a birnin Niamey lokacin zabe, 23 ga watan Fabarairu 2021. AFP - ISSOUF SANOGO

A jamhuriyar Nijar, Kungiyoyin fararen hula da dama ne sukayi kira jiya Asabar ga 'yan siyasa da gwamanati kan fifita bukatar tattaunawa, da kuma mutunta doka domin tinkirar halin rashin tsaro da bangarorin kasar da dama ke fama da shi, wanda ke hana fararen hula gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Talla

Yayin wani taron manema labarai jiya ranar Asabar, kungiyoyin fararen hular da farko sun yi kira ga bangarorin siyasa da su karfafa gwiwar fifita tattaunawa bayan rikicin da ya biyo baya zaben shugaban kasa, yayin da sukayi kira ga hukumomi don girmama 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma bukatan sakin wasu takwarorinsu dake tsare.

Wani mai fafutuka Sanoussi Mahamane ya yi tir da kame-kamen da akayi ba bisa ka'ida ba a cikin 'yan watannin nan, wanda yace akwai sama da masatasa 400 da aka kama ba bisa ka’ida ba.

'Yan kungiyar farar hula sun yi tir da tabarbarewar yanayin tsaro a yankunan Diffa, Tillabéri, Tahoua da kuma kan hanyar Agadez-Dirkou, gami da sace mutane da munanan hare-hare kan fararen hula. Suna kira ne da a kara tura jami'an tsaro kafin lamarin lokaci yak ure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.