Nijar-Juyin Mulki

Sojin da ya yi yunkurin kifar da gwamnatinn Nijar ya shiga hannu

Wasu sojojin kasar Nijar
Wasu sojojin kasar Nijar RFI / Sonia Rolley

'Yan sanda a Jamhuriyar Benin sun cafke Kaftin Sani Gourouza, sojin da ya yi yikurin kifar da gwamnatin Jamhuriyar Nijar a karshen watan Maris din da ya gabata,  tare da mika shi ga mahukuntan kasar.

Talla

Shi dai Kaftin Sani Gourouza ya kasance makitsin yinkurin juyin mulkin da bai cimma nasara ba,  wanda ya girgiza birnin Yamai a daren 30 zuwa 31 ga watan Maris din da ya gabata,  jajibirin rantsar da sabon shugaban kasar Mohammed Bazoum.

Tuni dai rundunonin  tsaron yan sanda da jandarmomin jamhuriyar Nijar da suka bada sammacin kama shi, suka tabbatar  da sahihancin labarin

Kafin kama shi dai yau da mako guda,  a ranar 20 ga wannan wata na Afrilu,  an bada labarin kama  wasu saojojin 2 da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin, da suka hada da mai mukamin , laftanar da mai mukamin Ajidan duk dai a kasar ta jamhuriyar Bénin kafin tankada keyarsu ga mahukunta a birnin Yamai.

Huldar aikin hadin guiwar jami’an tsaron kasashen 2 da ta bada damar cimma nasarar kama fandararen sojojin ta samu yabo da jinjina daga shuwagabanin rundunonin tsaron na Nijar da suka bada kambadar kama masu mutanen da suka arce zuwa kasar ta Benin .

Bayan cimma rashin nasarar yunkurin juyin mulkin a cikin jawabinsa na karshe da ya gabatar ga 'yan kasar shugaba Mahamadu Isufu ya yi tir da yinkuri, haka shi ma magajinsa Mahamadu Bazoum a ranar da aka rantsar da shi.

A yayin da 'yan adawa  suka bayyana lamarin a matsayin wasan yara da gwamnatin Mahamadu Isufu ta shirya domin kau da hankalinsu kan korafin rashin amincewa da zaben da hukumar zaben kasar CENI ta ce mahamadou Bazoum ya lashe a gaban dan takararsu Maman Usmane da ya ce shi ne ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.