Nijar - Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka sojojin Nijar 16

Sojojin Nijar dake aikin tsaro a yankin Tillabéry
Sojojin Nijar dake aikin tsaro a yankin Tillabéry © RFI

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce sojojin gwamnati 16 suka mutu sakamakon wani kwantar bauna da 'Yan bindiga suka musu a Yankin Tahoua dake kusa da iyakar Mali.

Talla

Sakatare Janar na 'Yankin Tahoua Ibrahim Miko ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yake cewa sakamakon harin sun samu gawarwakin soji 16 da kuma wasu 6 da suka jikkata, yayin da guda ya bata.

Miko yace ya halarci jana’izar Laftanar Maman Namewa, kwamandan rundunar dake sintirin da aka kaiwa hari.

Tserewar 'Yan ta'adda daga kurkuku

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijar ke sanar da kashe wasu da ake zargin 'Yan ta’adda ne guda 24 lokacin da suke kokarin tserewa daga inda aka kama su.

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum yayin ziyara a garin  Bosso, dake Diffa tare da rakiyar sojoji 17 ga watan Yuni 2016.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum yayin ziyara a garin Bosso, dake Diffa tare da rakiyar sojoji 17 ga watan Yuni 2016. © AFP - Issouf Sanogo

Sanarwar gwamnati tace mutanen sun dade suna shirya kai hari akan kasuwar Banibangou, amma sai aka tsegunatwa sojoji, kuma bayan musayyar wuta an kama 26 daga cikin su a ranar 28 ga watan jiya.

Sanarwar ma’aikatar tsaron tace yayin da ake shirin kwashe su zuwa Chinegodar dake da sansanin soji, sai suka nemi tserewa cikin dare, abinda ya sa aka harbe 24 daga cikin su.

Yankin iyakar kasashen uku na fama da rikici

Chinegodar da banibangou na Yankin Tillaberi dake kan iyakar Mali da Burkina Faso da Yan bindigar dake alaka da kungiyar Al Qaeda ko IS ke kai hari akai akai.

A ranar 15 ga watan Maris, Yan bindigar dake ikrarin Jihadi sun kashe mutane 66 lokacin da suka kai hari kan motar safa dake dauke da Yan kasuwa daga Banibangou kafin daga bisani suka kai hari kauyen Darey-Daye.

Wani kauye kan iyakar Mali da Nijar a watan Fabrairun  2020.
Wani kauye kan iyakar Mali da Nijar a watan Fabrairun 2020. AFP - MICHELE CATTANI

A ranar 2 ga watan Janairu, mutane 100 suka mutu sakamakon harin da aka kai kauyuka biyu a Yankin Mangaize dake Tillaberi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI