Nijar-Ta'addanci

Harin ta'addanci ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijar 15

Wasu sojojin Nijar masu yaki da Boko Haram.
Wasu sojojin Nijar masu yaki da Boko Haram. Getty Images

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tace Yan bindiga sun hallaka sojojin Kasar 15 a harin da suka kai musu a Yankin Tillaberi dake kusa da iyakar Mali. 

Talla

Gwamnatin kasar ta sanar da cewar harin na zuwa ne kwanaki 4 bayan kashe wasu sojoji 16 a Yankin.

Ma’aikatar tsaron Nijar tace maharan dauke da muggan makamai sun kai harin ne da jiya da rana akan sansanin sojin dake yaki da yan ta’adda na Almahou dake Intoussan kusa da garin Banibangou dake makotaka da kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.