Nijar-Faransa

Dakarun Faransa na da muhimmanci a yaki da ta'addanci - Bazoum

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Mohammed lokacin da ya ke karbar kwamandan rundunar Barkhane ta Faransa a birnin Yamai.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Mohammed lokacin da ya ke karbar kwamandan rundunar Barkhane ta Faransa a birnin Yamai. © Niger presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bayyana shirin ci gaba da aiki tare da dakarun Faransa wajen yaki da 'yan ta’adda a yankin Sahel.

Talla

Yayin da ya ke ganawa da shugaban rundunar sojin Barkhane Janar Marc Conruyt, shugaban ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi aiki tare da tsakanin sojojin Jamhuriyar Nijar da na rundunar Barkhane.

Ganawar ta tabo batun tsaron yankin Sahel da kuma hare hare bayan nan da ake samu akan dakarun Nijar, inda suka yi nazarin hanyoyin da za su dauka nan gaba da kuma aikin da za su yi tare.

Yayin da ya ke mayar da martani, Janar Conruyt ya bayyana cewar duk da ya ke ana samun nasara wajen yaki da 'yan ta’adda a yankin Sahel, amma yakin da su ke yi tare da rundunar G5 Sahel har yanzu akwai sauran aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI