Nijar - Muhalli

Matsalar bahaya a fili ta addabi mazauna sassan Jamhuriyar Nijar

Wani allo dake karin bayani kan shirin yaki da yin bahaya a fili a Jamhuriyar Nijar.
Wani allo dake karin bayani kan shirin yaki da yin bahaya a fili a Jamhuriyar Nijar. © UNICEF

Duk da illar dake tattare da bahaya ko kuma kashi a fili har yanzu wasu jama’a na aikata mummunar dabi'ar da aka dade ana yaki da ita domin kare lafiyar su.

Talla

Yanzu haka dai a Jamhuriyar a Nijar an sake samun bijirowar dabi’ar yin bahaya a fili, wadda ta mamaye kusan duk wasu filaye da basu da cikakken tsaro da makarantu da makabartu marasa kewaye na manyan biranen kasa.

Wakilinmu na Zinder Ibrahim Malam Tchillo ya duba halin da ake cikin kan matsalar kamar yadda za a ji cikin rahoton da ya aiko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI