Nijar-Ta'addanci

Rahoto kan kisan Sojojin Nijar 15 a kan iyakar kasar da Mali

Gawarwakin wasu Sojin Nijar da suka rasa rayukansu a harin ta'addanci ranar 13 ga watan Disamban 2019.
Gawarwakin wasu Sojin Nijar da suka rasa rayukansu a harin ta'addanci ranar 13 ga watan Disamban 2019. RFI/Moussa Kaka

‘Yan bindiga sun kashe Sojojin jamhuriyar Nijar 15 tare da raunata wasu akalla 4, a hari na baya-bayan nan da aka shekaranjiya talata cikin jihar Tillaberi da ke kusa da iyaka da kasar Mali .Wannan dai na nuni da cewa adadin sojojin kasar da suka rasa rayukansu sun tashi zuwa 31 a cikin kwanaki 4 da suka gabata. Daga Yamai, ga rahoton Rakia Arimi.