Nijar

Gwamnatin Nijar ta tura da karin sojoji jihar Diffa

Shugaban Nijar a yankin Bosso dake jihar Diffa
Shugaban Nijar a yankin Bosso dake jihar Diffa © AFP - Issouf Sanogo

Akalla farraren hula 4 hade da jami’an tsaro 4 suka rasa rayukan su a wani harin da mayakan boko haram suka kai birnin Diffa yammacin juma’a da ta gabata abinda ya haifar da musayar wuta tsakanin su da dakarun gwamnati.

Talla

Wani babban jami’in gwamnatin kasar ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar jami’an tsaro sun mayar da martanin da ya dace wajen anfani da manyan makamai tareda gundumuwar jiragen sama na soji.

Wasu sojojin dake yaki da yan Boko haram
Wasu sojojin dake yaki da yan Boko haram ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay

Jihar Diffa tayi ta fama da hare haren mayakan kungiyar boko haram tun daga shekarar 2015, ciki harda kazamin fadan da aka gwabza tsakanin mayakan da sojoji kusa da gadar Doutchi a watan Mayun bara. Yanzu haka akwai akalla Yan gudun hijira 300,000 a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI