Nijar-Boko Haram

Harin mayakan ISWAP ya kashe mutane 8 a jihar Diffa ta Nijar

Wasu Sojin Nijar a yankin Diffa mai fama da hare-haren ta'addanci.
Wasu Sojin Nijar a yankin Diffa mai fama da hare-haren ta'addanci. REUTERS/Joe Penney/

Akalla mutane 8 majiyoyin tsaro a Jamhuriyyar Nijar suka tabbatar da mutuwarsu a wani farmakin mayaka masu ikirarin jihadi a karshen makon jiya da ya faru akan iyakar kasar da Najeriya.

Talla

Majiyoyin tsaron na Jamhuriyyar Nijar sun ce jami’an tsaro 4 sun rasa rayukansu tare da wasu fararen hula 4 yayin farmakin na mayakan ISWAP tsagin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar IS.

Bayanai sun ce mayakan haye akan motoci 15 rike da manyan bindigogi ciki har da masu sarrafa kansu, sun farwa garin na Diffa akan iyakar Jamhuriyyar ta Nijar da Najeriya tare da kisan mutanen 8.

Ma’aikatar tsaron Nijar ta tabbatar da mutuwar mutanen 8 cikin sanarwar da ta fitar, inda ta bayyana kashe kaso mai yawa na mayakan jihadin baya ga nasarar kwato tarin makamai da alburusai ciki har da roka-roka da kuma wayoyin salula baya ga kwayoyin maye da sauran muggan miyagun kwayoyi.

Tun daga shekarar 2015 hare-hare a yankin Diffa ke tsananta wanda ya tilastawa mutane kusan dubu 200 tserewa da matsugunansu duk da yadda jihar ke dauke da ‘yan cirani kusan dubu dari 3 da hare-haren ‘yan ta’adda ya tilastawa barin matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI