Nijar-Tsaro

Makiyaya sun nemi hadin kan Nijar don magnce rashin tsaro

Shugaban Nijar Bazoum Mohamed tare da mambobin kungiyar makiyaya
Shugaban Nijar Bazoum Mohamed tare da mambobin kungiyar makiyaya © Niger Presidency

Kungiyar Makiyayan Jamhuriyar Nijar ta bukaci taimakon gwamnatin kasar wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke rutsa wa da ‘yayanta wajen gudanar da harkokinsu.

Talla

Kungiyar da ake kira ‘Bilital Maroobe‘ ta ziyarci shugaban kasa Bazoum Mohammed ne bayan wani taro da ta yi a birnin Yammai wanda ya tattauna matsalolin da ke addabar makiyaya da kuma nazari kan wani rahotan bincike.

Shugaban kungiyar Dodo Boureima ya ce taron nasu ya janyo masu ruwa da tsaki daga bangaren tsaro da makiyaya da kungiyoyin fararen hula da kuma sarakunan gargajiya.

Boureima ya ce, sun bukaci shugaba Bazoum da ya zama jakadansu a kungiyar ECOWAS da G5 Sahel da kuma kungiyar kasashen Afirka ta AU.

Shugaban kungiyar ya ce shugaban kasa Bazoum Mohammed ya amince da bukatarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.