Sudan - Nijar

Sudan ta nemi taimakon Nijar domin sasanta rikicin Kogin Nilu

Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021
Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021 © Niger Presidency

Kasr Sudan ta bukaci taimakon Jamhuriyar Nijar wajen warware rikicin Kogin Nilu dake gudana tsakanin kasar da Masar da kuma Habasha.

Talla

Ministar harkokin wajen kasar Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi ta bayyana bukatar lokacin da ta ziyarci shugaban Nijar Bazoum Mohammed a fadar sa dake birnin Yammai.

Fadar Bazoum tace Ministar tare da shugaban kasar sun tattauna batutuwa da dama da suka kunshi dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma harkokin da suka shafi kasashen Afirka da duniya baki daya.

Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021
Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021 © Niger Presidency

Al Mansoura ta bukaci shugaba Bazoum da yayi amfani da matsayin Jamhuriyar Nijar da kujerar da take da shi a Kwamitin Sulhu wajen sasanta takaddamar da ake cigaba da yi dangane da gina madatsar ruwan Habasha akan Kogin Nilu wanda zai hana Masar da Sudan ruwa.

Ministar ta kuma bukaci shugaban da ya kafa ofishin Jakadan Nijar a Khartoum domin bunkasa danganta tsakanin kasashen biyu, yayin da Sudan ke da nata ofishin a birnin Yammai.

Tawagar Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021
Tawagar Ministan harkokin wajen Sudan Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi tare da shugaba Bazoum Mohammed yayin ganawar su a Birnin Yammai ranar 01 ga watan Yunin shekarar 2021 © Niger Presidency

Sanarwar tace shugaba Bazoum Mohammed ya saurari bakuwar ta shi kuma ya bayyana shirin amfani da matsayin Nijar wajen tabbatar da zaman lafiya a Gabashin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.