Bazoum ya kaddamar da sabon shirin bada ilimi a Nijar

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed lokacin kaddamar da sabon shirin ilimi
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed lokacin kaddamar da sabon shirin ilimi © Niger Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya kaddamar da wani sabon shirin inganta harkar bada ilimi a cikin kasar wanda ake saran jama’ar kasar su ci moriyar sa.

Talla

Shirin bunkasa ilimin da aka yiwa lakabi da ’Niger Read‘ na samun tallafin Hukumar Cigaba ta Duniya da kuma Bankin Duniya wadanda zasu zuba kudin da ya kai Dala miliyan 140 ko kuma Cefa biliyan 75.

Gwamnatin Nijar tace shirin zai taimaka wajen inganta harkar koyarwa daga bangaren malamai da samar da makarantu ingantattu da kuma shugabancin a harkar bada ilimin baki daya, wanda ke karkashin shirin sabon shugaban kasa Bazoum na ganin ya samar da cigaba a fadin kasar.

Shugaba Bazoum Mohammed tare da manyan baki bayan kaddamar da sabon shirin ilimi
Shugaba Bazoum Mohammed tare da manyan baki bayan kaddamar da sabon shirin ilimi © Niger Presidency

Yayin jawabi wajen bikin shugaba Bazoum Mohammed ya bayyana harkar bada ilimi a matsayin daya daga cikin manyan kudirorin da gwamnatin sa ta saka a gaba.

Shugaban yace zasu cigaba da jajircewa wajen ganin sun cimma burin su duk da matsalolin tsaron da suke fuskanta wadda ke lakume makudan kudaden da suke samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.