Nijar-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace Sinawa a Nijar

Nijar na fama da hare-haren 'yan bindiga
Nijar na fama da hare-haren 'yan bindiga © Social News XYZ

Wasu 'yan bindiga a Jamhuriyar Nijar sun sace 'yan kasar China guda biyu da ke aikin hakar ma’adinai a yankin Tillaberi mai fama da tashin hankali, wanda ke iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso.

Talla

Gwamnan yankin Tillaberi Tidjani Ibrahim Katiela ya ce a daren ranar Lahadi 'yan bindigar suka dauke mutanen biyu a Mbanga.

Jihar Tilaberi na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.