Nijar-Ilimi

An fara samun raguwar fyade a Nijar

Dalibai yara mata a Jamhuriyar Nijar
Dalibai yara mata a Jamhuriyar Nijar © UNICEF Niger

A jamhuriyar Nijar, kokarin da sarkin Tasawa da ke Jihar Maradi ,Alhaji Mansur Kane Maigizo ke yi wajen kare ‘yaya mata daga matsalar muzgunawar da suke fuskanta, sarkin ya kafa wasu kwamitocin sa-ido sama da 200 a garuruwan da ke karkashin masarautarsa. A cikin gajeren lokaci da kaddamar da wannan shiri, an samu gagarumin sauyi ciki har da rage yi wa ‘yan mata fyade, daukar dawainiyar mata ta fannin kiwon lafiya, yayin da aka mayar da ‘yan mata sama da 300 makarantun Boko.

Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Salissou Issa

 

An fara samun raguwar fyade a Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.