Wasannin-Afirka

Yan wasan Nijar sun yi nasara a Afirka

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da daya daga cikin Yan damben kasar
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da daya daga cikin Yan damben kasar © Niger Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya karbi tawagar Yan wasan kasar da suka daga tutar kasar wajen lashe lambobin girma a wasannin da akayi a Dakar dake kasar Senegal da kuma Najeriya.

Talla

Tawagar Yan wasan ta lashe lambar zinare guda 2 da tagulla guda 3 a gasar takwando da akayi a Senegal, yayin da wasu kuma suka lashe lambar zinare guda biyu a gasar damben zamanin da akayi a Najeriya.

Daga cikin wadanda suka lashe lambar zinare a takwando akwai Abdoul Razak Issofou Alfaga a ajin masu nauyin kilo 57, sai kuma Balkissa Halidou da Ismael Garba da Mahamadou Maharana Tidjani da suka lashe tagulla a wasannin su.

Niger President with national athletes
Niger President with national athletes © Niger Presidency

A bangaren dambe kuma wadanda suka lashe lambar zinare akwai Moussa Sahabi Gado da Mohammed Yacouba da suka lashewa kasar zinare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.