Nijar - Lafiya

Mahukuntan Damagaram sun haramtawa masu magani furta kalaman batsa

Hoton magungunan gargajiya domin misali.
Hoton magungunan gargajiya domin misali. © Naijaloaded

Mahukunta a jihar Damagaram sun dauki matakin hana tallace tallacen magungunan gargajiya da ake furta kalamai na batsa da nuna hotunan al’aurar maza da mata, yayin da kuma masu tallan maganin ke amfani da lasifika mai karfin gaske a wuraren taruwar jama’a irinsu masallatai kasuwanni da tashoshi ko kuma cikin tituna hana.

Talla

An dauki matakin ne bayan da jama’a suka koka da irin kalaman da masu maganin ke furtawa.

Wakilinmu na Damagaram Ibrahim Malam Tchillo ya aiko da rahoto kan matakin hukumomin na Damagaram a Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.