Nijar

MDD ta nuna damuwa kan yawaitan hare-haren Boko Haram a yankin Diffa

Wasu dakarun jamhuriyar Nijar yayin atasaye a sansanin horas da su dake karkashin Amurka Flintlock dake garin Diffa.
Wasu dakarun jamhuriyar Nijar yayin atasaye a sansanin horas da su dake karkashin Amurka Flintlock dake garin Diffa. U.S. Africa Command - Spc. Zayid Ballesteros

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa dangane da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar dake kusa da kan iya Najeriya, inda kungiyoyin masu ikirarin jihadi ke ta kai munanan hare-hare tun daga shekarar 2015.

Talla

Cikin sanarwa da Hukumar agaji ta Majalisar ta fitar jiya Jumma’a tace, tsakanin watan Janairu zuwa Yunin da muke ciki, ankai hare-hare har sau tara cibiyoyin jami’an tsaro, masamman a Diffa da Maine -Soroa da Bosso, lamarin da tattabatar tabarbarewar al’amaru a tsawon iyakar kasar da Najeriya.

Ocha tace harin baya-bayan nan da aka kai ranar 5 ga watan Yuni da aka kai sansanin soji na SONIDEP kamfanin man fetur dake gabashin garin Diffa, ya raunata Jandarma daya, kafin maharani su yi awon gaba da motoci biyu bayan kone wasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.