Nijar - Ta'addanci

Kakakin Majalisar Dokokin Nijar Seini Oumarou ya tsallake rijiya da baya

Shugaban Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar Seini Oumarou, 2 ga watan Yuni shekarar 2008
Shugaban Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar Seini Oumarou, 2 ga watan Yuni shekarar 2008 AFP / Pius Utomi Ekpe

Hukumomin jamhuriyar Nijar na bincike kan farmakin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan gidan kakakin majalisar dokokin kasar Seini Oumarou, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daya daga cikin masu tsaron lafiyar sa, yayin da wani na biyu kuma ya jikkata.

Talla

Bayanai sun ce mahara biyu ne haye kan babura suka kai farmakin dauke da manyan bindigogi na zamani, a daren ranar Juma’a wayewar garin jiya Asabar, kamar yadda Osseini Salatou wani mai bashi shawara ya tabbatar.

Seini Oumarou, mai shekaru 70, ne yazo na uku a zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Disambar 2020, kafin ya marawa Mohamed Bazoum baya kuma yayi nasara.

Ma’aikatar cikin gidan Nijar ta tabbatar da kai harin a cikin wata sanarwa da yammacin Asabar, inda ta kara da cewa maharan biyu sun yi kokarin tuka wata motar 4x4 da ke tsaye a gaban gidan ba tare da samun nasara ba kafin su arce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.