NIJAR-TATTALIN ARZIKI

Nijar ta jaddada matsayin ta a kungiyar UEMOA

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da tawagar shugabannin kungiyar UEMOA a karkashin jagorancin shugaban ta Abdoulaye Diop
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da tawagar shugabannin kungiyar UEMOA a karkashin jagorancin shugaban ta Abdoulaye Diop © Niger Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya jaddada matsayin gwamnatin sa na cigaba da mutunta muradun kasar a cikin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma dake amfani da kudin bai daya na UEMOA lokacin da ya karbi shugaban ta Abdoulaye Diop a birnin Yammai.

Talla

Diop yace sun ziyarci shugaba Bazoum Mohammed ne domin taya shi murnar karbar ragamar mulkin kasar da kuma samun jagoranci wajen gudanar da ayyukan su a matsayin sa na shugaban kwamitin kasuwanci na shugabannin kasashen dake amfani da kudin UEMOA.

Shugaban yace hukumar sa ta samu gagarumar cigaba a cikin yan shekarun da suka gabata, saboda haka suna bukatar goyan baya da kuma jagoranci wajen ganin sun samu nasara.

Diop tare da shugaban Nijar Bazoum Mohammed sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi tsaro da tattalin arziki musamman a wannan lokaci da ake fama da annobar korona wadda ke cigaba da yiwa tattalin arzikin kasashe illa.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da shugaban UEMOA Abdoulaye Diop
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da shugaban UEMOA Abdoulaye Diop © Niger Presidency

 

Shugaban yace duk da raguwar kudaden da suke samu akwai alamu mai kyau na farfadowa da kuma shawo kan matsalar da suka fuskanta wajen yaki da annobar.

Diop yace zasu taimakawa kasashen dake cikin kungiyar wajen samun nasarar magance matsalolin da aka fuskanta sakamakon wannan annobar, yayin da ya yabawa Jamhuriyar Nijar dangane da hasken da ake fuskanta na habakar tattalin arzikin ta.

Bazoum yace kasashen UEMOA sun yi nasarar shawo kan matsalolin samar da abinci da kuma tinkarar matsalar tsaron da ta addabi yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI