Nijar-'Yan gudun hijira

Nijar za ta sauya wa 'yan gudun hijira dubu 20 matsuguni

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016.
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016. © ISSOUF SANOGO / AFP

Kimanin ‘yan gudun hijirar kasar Mali dubu 20 ne za a canza wa wurin zama daga wani sansani da ke Intikane da ke yankin Tillia a jihar Tawa kusa da iyaka da Mali, zuwa wani gari mai suna Akadany da ke cikin jihar Maradi a tsakiyar kasar.

Talla

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun yanke shawarar kwashe ‘yan gudun hijirar daga yankin na Tillia ne saboda dalilai na tsaro, musamman ma lura da yadda ake samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a yankin da ke daf da kan iyakar kasar da Mali.

Tuni dai aka dakatar da ayyukan jinkai ga ‘yan gudun hijirar dubu 20 da ke zaune a sansanin na Tillia kamar dai yadda mahukunta a yankin suka tabbatar.

Gwamnatin Nijar ta ce, ta yanke wannan shawara ce bayan tattaunawa da jami’an Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.

A cikin wannan shekara, ‘yan bindiga da ke tsallaka iyaka daga Mali sun kashe kimanin fararen hula 141 a garuruwan da ke yankin na Tillia, kuma tun a wannan lokaci ne gwamnatin Nijar ta ce za ta dauki matakin kare ‘yan kasar daga hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.