Nijar-Abinci

An sassauta farashin abinci a Nijar saboda barazanar yunwa

Kayayyakin abinci sun yi tsada a yankin Sahel
Kayayyakin abinci sun yi tsada a yankin Sahel Benson Ibeabuchi AFP

Majalisar Dinkin Duniya da wasu hukumomi daban-daban cikinsu har da Kungiyar Agaji ta OXFAM sun yi gargadi dangane da karuwar yunwa a wasu kasashe da ke Yankin Sahel. Tuni a Nijar aka fara yunkurin shawo kan matsalar ta yunwa.

Talla

A wani mataki na rage wa jama’a radadin hauhawan farashin abinci da ake fuskanta a duk duniya, a kasar Nijar an fara sayar da abinci a farashi mai rahusa ga talakawa na cikin garuruwan kasar musamman wadanda ke nesa da ke fama da tsadar abincin.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Ibrahim Malam Tchillo daga Damagaram na Jamhuriyar Nijar 

 

An sassauta farashin abinci a Nijar saboda barazanar yunwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.