NIJAR-ALGERIA

Nijar da Algeria sun kulla yarjejeniyar tsaro da tattalin arziki

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Shugaban Algeria Abdelmajjid Tebboune
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Shugaban Algeria Abdelmajjid Tebboune © Niger Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya kammala ziyarar aikin da ya kai kasar Algeria inda ya tattauna da shugaba Abdelmajid Teboune akan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu.

Talla

Ziyarar ta shugaba Bazoum Mohammed zuwa Algeria itace irin ta farko tun bayan hawar sa karagar mulki, inda suka tattauna batutuwa da dama da takwaran sa shugaba Abdelmajid Tebboune.

Shugabannin sun cimma matsaya akan batutuwa da dama da suka shafi tsaro da tattalin arziki da jin dadin jama’a da kuma horar da sojoji.

Dakarun Algeria na yiwa shugaban Nijar Bazoum Mohammed faretin ban girma a Algiers
Dakarun Algeria na yiwa shugaban Nijar Bazoum Mohammed faretin ban girma a Algiers © Niger Presidency

Daga cikin batutuwan da suka amince da su harda batun sake bude iyakokin kasashen biyu da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro da kuma barin Yan Nijar damar gudanar da ayyukan su a cikin kasar Algeria.

Ana saran bude iyakokin su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

President Abdelmajid Tebboune and Bazoum Mohammed in Algiers
President Abdelmajid Tebboune and Bazoum Mohammed in Algiers © Niger Presidency

Shugabannin sun kuma tattauna batun taimakawa Nijar da kayan leken asiri na soji domin yaki da Yan ta’adda da kuma horar da sojojin Nijar, tare da batun zuba jarin kamfanin man Algeria na Sonatrach wajen hakar mai a cikin Nijar.

Shugabannin sun kuma amince da shirin baiwa Algeria damar gina bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Nijar da Algeria domin kai shi nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.