Nijar-Algeria

'Yan Nijar na murna kan bude iyakarsu da Algeria

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Shugaban Algeria Abdelmajjid Tebboune
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Shugaban Algeria Abdelmajjid Tebboune © Niger Presidency

Al'ummar Nijar na cikin annashuwa da murna bayan gwamnati ta fitar da sanarwar da ke tabbatar da bude kan iyakar kasar da Algeria domin ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Nijar, Bazoum Mohamed ya ziyarci takwaransa na Algeria Abdoulaziz Teboun a makon jiya, inda suka cimma matsayar sake bude kan iyakar kasashen biyu.

Mazauna 'yan Agadez a Nijar sun dogara ne da kashi 70 na kayayyakin da ake shigo da su daga Algeria da suka hada da abinci irinsu Makaroni da Madara har ma da wasu abubuwan more rayuwa irin su motoci.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Omar Sanni daga Agadez

 

'Yan Nijar na murna kan bude iyakarsu da Algeria

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.