Nijar-Tattalin arziki

Korona ta yi raga-raga da arzikin Nijar- Bankin Duniya

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed.
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed. AFP - STEPHANE DE SAKUTIN

Bankin Duniya ya ce matsaloli masu nasaba da annobar korona sun yi matukar shafar tattalin arzikin Jamhuriyar Nijar, yayin da a hannu daya hare-haren ‘yan ta’adda suka hana mutane sakat a yankin Yammaci da kuma Kudu maso gabashin kasar.

Talla

Sanarwar da Bankin na Duniya ya fitar ta ce annobar korona da kuma rashin tsaro sun yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar tare da mayar da hannun agogo baya game da kokarin da kasar ta yi a fagen yakin da talauci cikin shekarun da suka gabata.

Rahoton ya ce tattalin arzikin Nijar wanda ya samu habaka ta kusan 6% a shekara ta 2019, ya rikito zuwa 3,6% a shehara ta 2020 saboda annobar ta korona da kuma rashin tsaro.

Bankin na Duniya ya ce, an samu karuwar mutane dubu 400 da suka shiga kangin talauci a kasar, yayin da rahoton ya yi hasashen samun karin wasu mutanen fiye da dubu 200 kafin karshen wannan shekara da za su fada kangin fatara.

Duk da cewa akwai karancin mutanen da suka kamu da cutar ta korona a kasar, amma mahukunta sun dauki matakan hana yaduwar cutar, yayin da aka rufe kasuwanni da dama saboda rashin tsaro tun shekara ta 2015.

To amma duk da haka Bankin na Duniya ya ce akwai yiyuwar tattalin arzikin kasar ya farfado a nan gaba, yayin da kasar ke fatan fara fitar da gurbataccen man fetur bayan kammala shimfida bututu da

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.