Nijar - Ta'addanci

Nijar: Mutane 14 sun mutu a kusa da iyakar Mali sakamakon harin ta'addanci

Wani sojan Jamhuriyar Nijar yayin aikin sintiri a Malam Fatori, dake yankin arewa maso gabashin kasar. Niger.
Wani sojan Jamhuriyar Nijar yayin aikin sintiri a Malam Fatori, dake yankin arewa maso gabashin kasar. Niger. Philippe Desmazes/AFP

Ma’aikatar cikin gidan jamhuriyar  Nijar ta tabbatar da mutuwar fararen hula 14  a harin da ‘yan bindiga a kan babura suka kai ranar shekaranjiya lahadi a wani kauye mai suna Wiye da ke gundumar Banibangou kusa da iyakar kasar da Mali.

Talla

Sanarwar ma’aikatar cikin gidan wadda aka fitar a yammacin jiya, ta ce 9 daga cikin mutanen an kashe su ne lokacin da suke noma a gonakinsu, 3 a cikin garin na Wiye sai kuma biyu wadanda maharan suka bindige a hanyarsu ta komawa gida daga gona.

Ma’aikatar cikin gidan ta kara da cewa an  tsaurara matakan tsaro, kuma ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata aika-aikar da zummar gurfanar da su gaban kuliya.

Banibangou na cikin inda aka sani a matsayin yankunan iyakoki 3 tsakanin Nijar, Burkina Faso da Mali, wanda tsawon shekaru kef ama da munanan hare hare daga kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaka da Al-Qaeda da IS.

A tsakiyar watan Maris, wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne sun kai hari a wannan wurin, a kan wata kasuwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 66.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI