Nijar

An kama manyan jami'ai a Nijar saboda almundahana

Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum
Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum AFP - STEPHANE DE SAKUTIN

A Jamhuriyar Nijar, yanzu haka jami’an tsaro na tsare da manyan jami’an Ma’aikatar Kudin Kasar da na Baitul-mali da dama, karkashin wani binciken sama da fadin cfa milyan dubu 8, kimanin Euro miliyan 12 da ake yi masu.

Talla

Bayanai da kafafen yada labaran kasar ta jamhuriyar Nijar, sun nuna cewa tuni mai shigar da kara na gwamnati a birnin Yamai ya bayar da umurnin tsare mutanen a gidan yari a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike dangane da lamarin.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya rawaito daya daga cikin jaridun kasar L’Enqueteur na cewa adadin mutanen da ake da hannu a wannan almundahna su 14 ne.

A tsakiyar wannan wata na Yuli ne shugaban kasar Mohamed Bazoum ya sanar da cewa, ya bayar da umurnin kaddamar da bincike dangane da zargin yin sama da fadi da dukiyar jama’a a Baitul-malin kasar,  bayan da aka rawaito cewa shugaban Sashen Kula da Ayyukan Sufuri a fadar shugaban kasar ya fitar da makudan kudade ba a kan ka’ida ba.

Wadannan kudade da ake zance cfa miliyan dubu 12, an fitar da su ta barauniyar hanya ce tsakanin shekara ta 2017 zuwa 2021.

Yanzu haka dai akwai wani zargin karkata kudaden da yawansu ya dai Euro miliyan 50 da aka ware don sayen makamai a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.