'Yan bindiga sun kashe mutane 18 a kauyen Dey Koukou dake Nijar

Rundunar yan Sandar Nijar cikin aiki
Rundunar yan Sandar Nijar cikin aiki Boureima HAMA AFP/Archivos

‘Yan bindiga a kan babura sun kai hari tare da kashe fararen hula 18 a kauyen Dey Koukou da ke yankin Banibangou kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar da Mali.

Talla

Kauyen Alou Koira ne, wanda ke da nisan kimanin kilomita 20 daga yankin na Banibangou maharan da suka zo kan babura suka haura.  An kashe mutane 18 a kauyen da gonakan da ke kewaye.  Akalla mazauna kauyen 3 suka samu rauni.

Jami'an tsaro a wasu yankunan  da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery
Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery RFI

 A cewar majiyoyi da dama, mutanen da ke dauke da makamai a baya sun kasance a kauyen Deykoukou inda suka yi kokari tafiya da dabbobi sai dai basu ci nasara ba. Ko a ranar lahadin da ta gabata ‘yan bindiga sun kashe fararen hula 14 a wani kauye da ke yankin. Mazauna kauyen sun hangi kuma wani rukunin maza dauke da makamai tsakanin kauyukan Farka da Dingazi Banda, a cikin wani daji .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI