Nijar-Ta'addanci

Mayaka masu ikirarin jihadi sun kashe masallata 10 a jihar Tillaberi ta Nijar

Yankin Tillabéri a Jamhuriyyar Nijar.
Yankin Tillabéri a Jamhuriyyar Nijar. © RFI

Majiyoyin tsaro a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da wani harin mayaka masu ikirarin jihadi da ya hallaka fararen hula 10 lokacin da su ke tsaka da sallah a wani kauye na jihar Tillaberi da ke yammacin kasar gab da kan iyaka.

Talla

Hukumomin Nijar sun ce harin ya faru ne tun a ranar Litinin din da ta gabata inda mayakan suka shiga garin haye a babura tare da bude wuta kan mutane wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

Kauyukan jihar Tlaberi da ke gab da kan iyakar Jamhuriyyar Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso masu fama da hare-haren kungiyoyin da ke ikirarin jihadi, su ne kan gaba yanzu haka a kasar ta yankin Sahel a jerin yankunan da ke fuskantar tashe-tashen hankula.

Wani jami’i a garin Banibangou ya shaida wa kamfanin dilancin labaran Faransa cewa maharan bisa babura sun isa garin ne a yayin da ake tsaka da sallar magriba, inda suka iske wadanda abin ya rutsa da su a masallaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI