Nijar-Ilimi

Nijar na shirin kawo karshen tsarin malunta karkashin kwantiragi

Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum. Eduardo Munoz

A kokarin da ta ke na inganta harkar bayar da ilimi a fadin kasa, Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa za ta kawo karshen tsarin aikin malanta a karkashin kwantiragi. An bayyana haka ne bayan wani zaman taro kan harkar ilimi da shugaban kasar Bazoum Mohammed ya jagoranta, yayinda malaman kwantiragin ke bayyana shakku duk da rashin sanin yadda sabon shirin na gwamnatin zai kasance. Wakilinmu na Damagaram Ibrahim Malam Tchillo na dauke da rahoto.